IQNA

Gobe Za A Kallama Gasar Kur'ani Ta Larduna A Kasar Turkiya

16:11 - June 07, 2009
Lambar Labari: 1788205
Bangaren kasa da kasa: Idan Allah ya kai mu gobe ne za a kammala gasar kur'ani ta larduna a kasar Turkiya, wadda ta samu halartar mafi yawan makaranta da mahardata kur'ani da ke fadin kasar a cikin lardunansu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sondakika na kasar Turkiya cewa; gobe ne za a kammala gasar kur'ani ta larduna a kasar Turkiya, wadda ta samu halartar mafi yawan makaranta da mahardata kur'ani da ke fadin kasar a cikin lardunansu. Bayanin ya ci gaba da cewa babban limamin masallacin juma'a na birnin shi ne babban bako da zai jagoranci mika takardun shedar kammala hardar kur'anin ga mahardatan da za su halarci wurin taron.Daya daga cikin wadanda suka shirya gudanar da wannan taro karkashin cibiyar kula da harkokin addini musulunci ta birnin ya bayyana cewa, manufar hakan ita ce karfafa gwiwar mahardatan domin ci gaba da bayar da himma wajen hardar.

416623







captcha