IQNA

Za A Fara Gudanar Da Taro Kan Ilimin Addinin Musulunci A Faransa

16:13 - June 07, 2009
Lambar Labari: 1788207
Bangaren kasa da kasa: Za a fara gudanar da zaman taro na shekara-shekara kan ilimin addinin addinin musulunci a nahiyar turai, wanda a wannan karo za a gudanar da shi ne a kasar Faransa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Saphirnews cewa; Za a fara gudanar da zaman taro na shekara-shekara kan ilimin addinin addinin musulunci a nahiyar turai, wanda a wannan karo za a gudanar da shi ne a kasar Faransa. Cibiyar kula da harkkin ilimin addinin musulunci a nahiyar turai ce ta dauki nauyin gudanar da shirin kamar yadda ta saba yi a sauran shekaru. Daga cikin wadanda za su halarci taron kuwa akwai masana kan harkkin ilimi daga kasashn musulmi, da kuma malaman jami'a musulmi daga sassa daban-daban na kasashen nahiyar turai.


416546



captcha