Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga reshensa na kasar Pakisan cewa; babban limamin juma'a na birnin Miryur na kasa pakistan ya bayyana cewa; Daya daga cikin siffofin da Imam Khomeini mu'assasin juyin juya halin musulunci a Iran ita ce rashin tsoron makiyansa, tare da fuskantarsu ba tare da wani shayi ba, tare da dogaro da Allah madaukakin sarki. Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar juma'a a gaban dubban masallata a lokacin da yake gabatar hudubar sallar juma'a. Ya ce dogar da Allah shi ne babban sirrin duk wata nasara da Imam Khomeini ya samu a cikin gwagwarmayarsa, tun daga lokacin da yake gwagwarmaya har zuwa samun nasarar juyin juya halin musulunci a Iran.
416483