IQNA

Ayyukan Imam Khomeini (RA) Samfuri Ne Na Adalcin Musulunci

23:42 - June 08, 2009
Lambar Labari: 1788410
Bangaren kasa da kasa: marigayi Imam Khomeini ya kasance babban samfuri na adalci a mahangar addinin Musulunci, kama daga ayyukansa har zuwa dabi'unsa da maganganunsa, da kuma yadda ya tafiyar da al'umma a lokacin rayuwarsa, kafin samun nasar juyin juya halin Musulunci da kuma bayan samun nasar juyin.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da daya daga cikin jagororin mabiya addinin Musulunci da ke kasar Belgium dangane da rayuwar marigayi Imam Khomeini ya bayyana cewa; marigayi Imam Khomeini ya kasance babban samfuri na adalci a mahangar addinin Musulunci, kama daga ayyukansa har zuwa dabi'unsa da maganganunsa, da kuma yadda ya tafiyar da al'umma a lokacin rayuwarsa, kafin samun nasar juyin juya halin Musulunci da kuma bayan samun nasar juyin. Ya ci gaba da cewa babban mabudin dukkanin nasara da Imam ya samu a cikin harkokinsa na neman ilimi da gwagwarmaya da kafa gwamnatin Islama a Iran, ba wani abu ba ne illa dogaronsa da Allah madaukakakin sarki, wanda kuma rayuwarsa cike take da abubuwan koyi ga dukkanin musulmi da ma 'yan adam baki daya.

417230




captcha