Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani zaman taro a kasar Swedden dangane da cika shekaru 61 da yahudawan sahyuniya suka mamaye palastinu, wanda cibiyar kula da harkokin musulmi ta kasar ta shirya gudanarwa a birnin Bornbry, birni na biyu a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ma'a cewa; An gudanar da wani zaman taro a kasar Swedden dangane da cika shekaru 61 da yahudawan sahyuniya suka mamaye palastinu, wanda cibiyar kula da harkokin musulmi ta kasar ta shirya gudanarwa a birnin Bornbry, birni na biyu a kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa daya daga cikin wadanda suka shirya gudanar da wannan taro Safi Khalid ya bayyana cewa; an fara gudanar da wannan taro ne domin kara tunatar da al'ummomin duniya dangane da halin da masallacin Qods mai alfarma yake ciki, da kuma barazanar da yake fuskanta daga yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi, yayin da kuma Isra'ila ke ci gaba da mamaye yankunan palastinawa da ke gabacin Qods.
417248