Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani taron girmama wasu mata 150 mahardata kur'ani mai tsarki a kasar hadaddiyar daular larabawa, wanda cibiyar kula da iyali ta kasar ta shirya gudanarwa a birnin Zaid na kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran wam cewa; An gudanar da wani taron girmama wasu mata 150 mahardata kur'ani mai tsarki a kasar hadaddiyar daular larabawa, wanda cibiyar kula da iyali ta kasar ta shirya gudanarwa a birnin Zaid na kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar manyan mutane daga sassa daban-daban na kasar, da suka hada da malama Fatimah Saif Mazru'I babbar darata a cibiyar kula da harkokin iyali ta kasar gami da wasu manyan jami'ai daga ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar, da kuma jami'ai daga ma'aikatun kula da al'adu da kuma zamantakewa jama'a. Fatima Mazru'i t ace gudanar da wannan taro yana da matukar muhimmanci, domin kuwa zai kara karfafa mata wajen mayar da hankali ga kur'ani mai tsarki.
417222