IQNA

Gwagwarmayar Imam Khomeini (RA) Ta Kawo Canji A Siyasar Duniya

23:41 - June 08, 2009
Lambar Labari: 1788415
Bangaren kasa da kasa: A lokacin da Imam Khomeini ya mike domin tunkarar zalunci da dukkanin imaninsa da Allah madaukakin sarki, da kuma nasarar da ya samu bayan fuskantar wahalhalu a kan tafarkin gaskiya, da yadda ya tabbatar da adalci a bayan kawar da tsarin zalunci da babakere, hakan ya kawo gagarumin canji a siyasar duniyarmu ta yau.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga babban daraktar cibiyar ahlul bait reshen kasar Holland cewa; A lokacin da Imam Khomeini ya mike domin tunkarar zalunci da dukkanin imaninsa da Allah madaukakin sarki, da kuma nasarar da ya samu bayan fuskantar wahalhalu a kan tafarkin gaskiya, da yadda ya tabbatar da adalci a bayan kawar da tsarin zalunci da babakere, hakan ya kawo gagarumin canji a siyasar duniyarmu ta yau. Ya ci gaba da cewa babban mabudin dukkanin nasara da Imam ya samu a cikin harkokinsa na neman ilimi da gwagwarmaya da kafa gwamnatin Islama a Iran, ba wani abu ba ne illa dogaronsa da Allah madaukakakin sarki, wanda kuma rayuwarsa cike take da abubuwan koyi ga dukkanin musulmi da ma 'yan adam baki daya.

417114

captcha