IQNA

An Tarjama Littafin Imam Khomeini (RA Yunkurin Ashura Da Harshen Albaniya

23:42 - June 08, 2009
Lambar Labari: 1788417
Bangaren kasa da kasa: A daidai lokacin da ake gudanar da taruka na tunawa da cika shekaru ashirin da rasuwar marigayi Imam Khomeini, an kaddamar da wani littafinsa mai suna Imam Hussaini (AS) a ranar Ashura, wanda aka tarjama zuwa harshen Albaniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Albaniya ya habarta cewa; A daidai lokacin da ake gudanar da taruka na tunawa da cika shekaru ashirin da rasuwar marigayi Imam Khomeini, an kaddamar da wani littafinsa mai suna Imam Hussaini (AS) a ranar Ashura, wanda aka tarjama zuwa harshen Albaniya. Bayanin ya ci gaba da cewa ofishin jakadancin jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke kasar Albaniya ne ya dauki nauyin tarjama littafin na marigayi Imam Khomeini, wanda aka kaddamar a ranar da ya cika shekaru ashirin cif da yin kaura daga gidan duniya zuwa ga ubangijinsa. Da dama daga cikin al'ummomin musulmi da ke kasar Albaniya sun nuna matukar jin dadinsu dangane da fassara wannan littafi da aka yi zuwa yarensu, ta yadda hakan zai saukaka musu wajen fahimtar manufofin addini Musulunci da tarihinsa.

416598



captcha