IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Taro Kan Kur'ani A Kasar Canada

17:18 - June 09, 2009
Lambar Labari: 1789000
Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani zaman taro mai taken kare harshen kur'ani mai tsarki a kasar Canada, wanda za a fara gudanarwa a birnin montrol na kasar, daga bisani kuma a gudanar da bangare na biyu a birnin Tronto babban birnin kasar ta Canada.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na sabeel education cewa; Za a gudanar da wani zaman taro mai taken kare harshen kur'ani mai tsarki a kasar Canada, wanda za a fara gudanarwa a birnin montrol na kasar, daga bisani kuma a gudanar da bangare na biyu a birnin Tronto babban birnin kasar ta Canada. Babbar cibiyar kula da harkokin musulmi ta kasar Canada wato sabeel, ita ce ta shirya gudanar da wannan zaman taro, wanda zai samu halartar masana da malaman addinin musulunci daga sassa daban-daban na kasar. Babbar manufar gudanar da taron dai ita ce kara fadakar da musulmi kan muhimmancin riko da koyarwar kur'ani mai tsarki, wanda kuma hakan zai taimaka wajen bayar da kyakkyawar tarbiya da misali ga sauran matasa musulmi.

417845





captcha