IQNA

An Fara Bayar Da Horo Kan Karatu Da Hardar Kur'ani A Sharjah

17:13 - June 09, 2009
Lambar Labari: 1789002
Bangaren kasa da kasa: A karon farko an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan harda da kuma karatun kur'ani mai tsarki a birnin Sharjah na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda kuma shirin ya kebanci matasa ne.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Hadaddiyar daular larabawa WAM cewa; A karon farko an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan harda da kuma karatun kur'ani mai tsarki a birnin Sharjah na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, wanda kuma shirin ya kebanci matasa ne. Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar kula da harkokin matasa ta birnin sharjah ce ta shirya wannan bayar da horo na musamman ga matasan birnin, kuma shirin zai dauki tsawon wata biyu ana gudanar da shi, yanzu haka dai akwai matasa kimanin 35 da suka fara samun wannan horo, wanda kuma za su kammala na su samun horon kafin watan Ramadan mai zuwa.


417780








captcha