Bangaren kasa da kasa: An shiga bangaren karshe na gasar kur'ani mai girma ta kasa da ake gudanarwa a kasar Saudiyya, ana gudanar da bangaren karshen ne na gasar karatun kur'ani da kuma harda a dakin gudanar da taro na oten din birnin Kasim.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ma'aikatar kula da harkokin ilimi ta kasar saudiyya cewa; An shiga bangaren karshe na gasar kur'ani mai girma ta kasa da ake gudanarwa a kasar Saudiyya, ana gudanar da bangaren karshen ne na gasar karatun kur'ani da kuma harda a dakin gudanar da taro na oten din birnin Kasim. Bayanin ya ci gaba da cewa bangaren karshe na gasar ana gudanar da shi ne a bangaren harda da kuma karatun kur'ani gami da ilimin ka'idojin karatun kur'ani wato tajwidi, inda dukkanin mahalrta gasar da suke karawa da juna matasa ne masu karatu a makarantun sakandare, adadinsu kuma ya kai matasa 120 daga sassa daban-daban na kasar.
417760