IQNA

Riko Da Addini Shi Ne Makamin Tunkarar Duk Wata Gurbatacciyar Akida

17:17 - June 09, 2009
Lambar Labari: 1789009
Bangaren kasa da kasa: Babban jami'I da ke kula da harkokin addini a ma'akatar harkokin cikin gida ta kasar Turkiya Faruk Chelik ya bayyana cewa; yin riko da addini shi ne babban makamin tunkarar duk wata gurbataciyar akida.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Star na kasar turkiya cewa; Babban jami'I da ke kula da harkokin addini a ma'akatar harkokin cikin gida ta kasar Turkiya Faruk Chelik ya bayyana cewa; yin riko da addini shi ne babban makamin tunkarar duk wata gurbataciyar akida. Ya ci gaba da cewa a tsawon tarihin mutanen da suka samu ilmin addini da kyakkyawar tarbiya irin ta addini sun e suke zama mutane na gari a cikin kowace al'umma, a kan ya ce yin riko da koyarwa irin ta addini hakan ita ce sahihiyar hanya wajen kawar da batattun dabi'u da ke gurbata rayuwar matasa da dabi'unsu a cikin rayuwa ta zamantakewa;

417732






captcha