IQNA

An Bude Cibiyar Gudanar Da Bincike Kan Addinai A Kasar Turkiya

17:17 - June 09, 2009
Lambar Labari: 1789012
Bangaren kasa da kasa; An bude wata cibiya ta kasa da kasa domin gudanar da bincike kan addinai da harkokin al'adun al'ummomi a birnin Gaziosman da ke cikin gundumar Istanbul fadar mulkin kasar ta Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran haber34 cewa; An bude wata cibiya ta kasa da kasa domin gudanar da bincike kan addinai da harkokin al'adun al'ummomi a birnin Gaziosman da ke cikin gundumar Istanbul fadar mulkin kasar ta Turkiya. A lokacin da ake gudanar da bukin bude cibiyar magajin garin gazi osman pasha ya bayyana cewa; kowace al'umma na da wata lama da ake gane tad a al'adunta, kuma wajibi a girmama al'adu da akidun kowace al'umma domin tabbatar da fahimtar juna da zaman lafiya da kuma abkantaka mai dorewa. Y ace yana fatan al'ummomin duniya za su amfana da wannan cibiya wajen sanin al'adu daban-daban da addinai da kuma yin nazarinsu.

417701






captcha