IQNA

An Kawo Karshen Gasar Kur'ani A Yankin Anatoli Na Turkiya

17:16 - June 09, 2009
Lambar Labari: 1789015
Bangaren kasa da kasa: An kawo karshen gasar karatun kur'ani da aka gudanar a birnin Anatoli na kasar turkiya, a babban masallacin Haj Sharif da ke birnin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; An kawo karshen gasar karatun kur'ani da aka gudanar a birnin Anatoli na kasar turkiya, a babban masallacin Haj Sharif da ke birnin. Gasar ta samu halartar malaman addinin musulunci daga sassa daban-daban na kasar Turkiya, daga cikin hard a malaman addini da na makaratun Islamiyya da ke birnin Istanbul. An bayar da kyautuka na musamman ma ga wadanda suka samu matsayi na daya da mai matsayi na biyu da kuma wanda ya samu zuwa a matsayi na uku, dukkansu sun fit one daga garuruwa daban-daban da ke cikin gundumar Anatoli.

417671




captcha