Said Muhammad Huseini daya daga cikin mambobi a komitin malummai na ahlulu sunna a wata tattauanawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ya bayyana cewa: rashin hadin kai zai iya haddasa wani yaki a tsakanin mazhabobi da kawo babban gibi ga manufofi da alfanon addini da duniya baki daya. Yayi nuni da aya ta 103 a cikin suratul Umrana da ke bayani kan mu tuna da ni'imar da Allah ya yi mana inda kuka kasance makiyan juya amma sai aka sanya soyayya a tsakanin juna da cewa; wannan aya tana bayani kan falalar Allah a gare mud a muhimmancin nuna kauna da soyayya ga junanmu.
417840