Bangaren kasa da kasa; Ana shirin aiwatar da wani shiri na hada mabuta kur'ani a kasar hadaddiyar daular larabawa da aka baiwa take duniyar ma'abuta kur'ani mai tsarki, wanda cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci da ayyukan alkhairi ta kasar ta dauki nauyin gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran wam na hadaddiyar daular larabawa cewa; Ana shirin aiwatar da wani shiri na hada mabuta kur'ani a kasar hadaddiyar daular larabawa da aka baiwa take duniyar ma'abuta kur'ani mai tsarki, wanda cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci da ayyukan alkhairi ta kasar ta dauki nauyin gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban cibiyar kula da harkokin kur'ani na kasar ya bayyana cewa; wannan shirin yana dauke da alfanu ga dukkanin musulmi, musamman ma ma'abuta kur'ani daga cikinsu, domin kuwa wannan shiri zai taimaka wajen sanin dukkanin harkokin da ake gudanarwa a duniyar musulmi da suka shafi kur'ani mai tsarki.
418186