Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani taron tattaunawa tsakanin addinai da kuma tasirinsu wajen bayyana kimar dan adam da rawar da suke takawa wajen kare hakkokinsa da saita tunaninsa wajen samun kyawan dabi'u, wanda za a gudanar a birnin Geneva na kasar Switzerland.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Nasij cewa; Za a gudanar da wani taron tattaunawa tsakanin addinai da kuma tasirinsu wajen bayyana kimar dan adam da rawar da suke takawa wajen kare hakkokinsa da saita tunaninsa wajen samun kyawan dabi'u, wanda za a gudanar a birnin Geneva na kasar Switzerland. Taron wanda za a gudanar karkashin kulawar bangarorin Saudiyya da kuma Spain, sarkin Saudiyya Abdullah Bin Abdulaziz shi ne zai shiga gaba wajen jagorantar zaman taron. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai mayar da hankali ne wajen muhimmancin da ke tattare da tattaunawa da kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai, ta yadda hakan zai taiamaka wajen samun zaman lafiya a duniya.
418248