IQNA

Taron Mai Taken Mace Hasken Rayuwa A Labanon

17:18 - June 10, 2009
Lambar Labari: 1789710
Bangaren ilimi da fasaha: taro kan mace hasken rayuwa za a gudanar da shi a kasar labanon kan zagayowar ranar haifuwar fiyayyar halitta Fatima Zahra (AS) kuma ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar labanon net a shirya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; a lokacin gudanar da wannan taro za a yi bayani kan yanayin siyasa da al'adu gami da zamantakewar mata a kasar Labanon da kuma yadda suka samu ci gaba ta fuskar ilimi.Daga cikin wadanda za su gabatar da jawabai a gurin wannan taro akwai Ma'asuma Firuzi masana kuma kwararriya mai bincike kan lamuran da suka shafi mata har ila yau akwai Shida Nikuravid mai bincike kan abubuwa da suka shafi islama.

418314


captcha