Bangaren adabi da al'adu: Ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar kanada ne ya daukin nauyin buga wannan littafi kan Imam Khomeini ® rayuwarsa,tasirinsa da kuma tunaninsa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: wannan littafi an wallafa shi a daidai wannan lokaci na ci gaba da juyayin cika shekaru ashirin da rasuwar Imam Khomeini ® muassasin juyin juya halin musulunci a Iran.har ila yau wannan littafi ya kumshi rayuwar wannan bawon Allah da yadda ya rayu rayuwa mai tsabta da kuma yadda yayi tasiri a zamantakewar jama'a da ci gabansu da kuma uwa uba yadda tunaninsa da hangen nesansa ya taka rawar gani a tsakanin al'ummomi daban daban na duniya .
417823