Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da gasar hardar kur'ani da ta kebanci mata a fadin kasar Libya, wadda hukumar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar da ke da cibiya a birnin Tripoli fadar mulkin kasar ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alfajr cewa; An fara gudanar da gasar hardar kur'ani da ta kebanci mata a fadin kasar Libya, wadda hukumar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar da ke da cibiya a birnin Tripoli fadar mulkin kasar ta shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa an fara gudanar da gasar ne jiya, kuma za a ci gaba da gudanar da ita har zuwa tsawon kwanaki shida a nan gaba, inda mata 45 dukkaninsu mahardata kur'ani suke karawa da juna. Ana gudanar da gasar a fagagen harda da kuma karatu gami da ka'idojin karatu wato tajwidi, inda daga karshe za a gudanar da bangare na karshe, inda za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka lashe gasar.
418712