Bangaren kasa da kasa; Wani malamin yahudawan sahyuniya mai tsattsauran ra'ayi a Amurka Manis Faridman, ya bayyana cewa kashe palastinawa maza da mata tsoffi da kanan yara daga cikinsu, gami da rushe gidajensu da kuma rushe wurare masu tsarki na musulmi da ke cikin palastinu, shi ne hanyar zaman lafiya ga yahudawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; Wani malamin yahudawan sahyuniya mai tsattsauran ra'ayi a Amurka Manis Faridman, ya bayyana cewa kashe palastinawa maza da mata tsoffi da kanan yara daga cikinsu, gami da rushe gidajensu da kuma rushe wurare masu tsarki na musulmi da ke cikin palastinu, shi ne hanyar zaman lafiya ga yahudawa. Manis Farid man ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Amurka, inda ya bayyana cewa dukkanin abin da yahudawan sahyuniya suke aikatawa kan palastinawa shi ne daidai, domin kuwa hakan shi ne zai ba su damar wanzuwa tare da wanzuwar daularsu ta yahudawa, kuma hakan ba zai yuwu ba har sai an kawo karshen palastinawa.
418770