IQNA

An Fara Gina Wata Babbar Cibiyar Kur'ani A Kasar Turkiya

23:01 - June 11, 2009
Lambar Labari: 1789786
Bangaren kasa da kasa; An fara gina wata babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani mai girma a gundumar Cukurova da ke lardin Adana na kasar Turkiya, inda bikin dora tubalin ginin cibiyar ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin kasar ta Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran adanmediya cewa; An fara gina wata babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani mai girma a gundumar Cukurova da ke lardin Adana na kasar Turkiya, inda bikin dora tubalin ginin cibiyar ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin kasar ta Turkiya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan cibiya za ta taka rawa wajen kula da harkokin kur'ani a fadin kasar, da hakan ya hada da shirya gasar karatun kur'ani, horar da matasa karatun kur'ani da ka'idojinsa gami dad a gina makarantu da dai sauransu, wanda hakan babbar nasara ce ga musulmi masu sha'awar kur'ani da karatunsa.

418764


captcha