IQNA

An Fara Gudanar Da Taro Domin Tara Kudaden Taimakon Addini A Algeria

23:04 - June 11, 2009
Lambar Labari: 1789787
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da zaman taro na kasa da kasa domin tara kudaden taimakon addinin Musulunci a birnin Kustantin na kasar Algeria, wanda kuma wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannan taro.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar elmojahid cewa; An fara gudanar da zaman taro na kasa da kasa domin tara kudaden taimakon addinin Musulunci a birnin Kustantin na kasar Algeria, wanda kuma wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannan taro. Taron zai kwashe kwanaki uku ana gudanar da shi, Yusuf Azwaza da ke jagorantar zaman taron ya bayyana cewa akwai masana dad a malamai daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da suke halartar taron, haka nan kuma wasu daga cikin jami'an gwamnatin kasar musamman ma daga ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar suna halartar taron, inda ake ci gaba da tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin tattalin arziki da kuma yadda taiamaka wa kasashen musulmi masu rauni.

418817

captcha