Bangaren fikira; Shugaban cibiyar kula da harkokin bincike da nazari ta daliban jami'oin duniyar musulmi ya bayyana cewa; za a bijiro da maganganun Imam Khomeini(RA) dangane da duniyar musulmi da kuma ma'anar hakan, domin yin nazari kansu a wajen taron.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Shugaban cibiyar kula da harkokin bincike da nazari ta daliban jami'oin duniyar musulmi ya bayyana cewa; za a bijiro da maganganun Imam Khomeini(RA) dangane da duniyar musulmi da kuma ma'anar hakan, domin yin nazari kansu a wajen taron. Bayanin ya ci gaba da cewa akwai littafai da jabai da Imam Khomeini ya gabatar a lokacin rayuwarsa dangane da ma'anar duniyar musulmi, kuma wadanne kasashe ne suka shiga cikin duniyar musulmi, a cikin taswirar kasa daga ina zuwa ina ne taswirar duniyar musulmi, wanda kuma a cewar shugaban kwamitin, daliban jami'oi na kasashen ya kamata su san hakan. Ya kara da cewa daga cikin jawaban da kuma littafan nasa da suke dauke da irin wadannan bayanai, akwai wadanda aka tarjama zuwa harsuna daban-daban na duniya, kuma za a raba su ga daliban.
418981