Bangaren adabi; Bisa kididdigar baya-bayan da aka gudanar, an tabbatar da cewa sama da littafai dubu 60 ne na addinin Musulunci ke cikin dakin karatu na kasa da ke birnin Tehran, wanda ke bayani kan samun masaniya dangane da addinin Musulunci da kuma koyarwarsa a cikin dukkanin bangarori na rayuwar dan adam.
Kamfanin dillancin labaran Ikna yanakalto daga bangaren kula da hulda da jama'a na cibiyar kula da harkokin dakunan karatu na kasa cewa; Bisa kididdigar baya-bayan da aka gudanar, an tabbatar da cewa sama da littafai dubu 60 ne na addinin Musulunci ke cikin dakin karatu na kasa da ke birnin Tehran, wanda ke bayani kan samun masaniya dangane da addinin Musulunci da kuma koyarwarsa a cikin dukkanin bangarori na rayuwar dan adam. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin dakin karatun akwai littafai miliyan daya da dubu dari takwas da satin da daya, wadanda ake ci gaba da adana su a cikin wannan katafaren dakin karatu domin amfanin masu gudanar da bincike da nazarai a bangarori daban-daban na ilimi.
419048