Bangaren kasa da kasa; An kammala wani bayar da horo da aka gudanar a kasar hadaddiyar daular larabawa dangane da muhimmancin yin nazari kan sabbin ilmomi da mahangar kur'ani a kansu, wanda cibiyar kula da harkokin addini ta kasar ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar albayan cewa; An kammala wani bayar da horo da aka gudanar a kasar hadaddiyar daular larabawa dangane da muhimmancin yin nazari kan sabbin ilmomi da mahangar kur'ani a kansu, wanda cibiyar kula da harkokin addini ta kasar ta shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron yana samun halartar manyan malamai daga sassa daban-daban na kasashen musulmi, daga cikin malaman kuwa har da malaman mabiya mazhabar shi'a daga cikin masana da malamai 600 da suke halartar zaman taron. Za a kwashe kwanaki biyu ana gudanar da wannan zaman taro, da nufin samar da hanyoyin da suka d ace daga wajen warware matsaloli da dama da duniya ke fuskanta a mahamnagar kur'ani.
419414