Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani shiri na bayar da horo ga mahardata kur'ani a zirin Gaza, wanda ya kebanci mata da suka hada da daliban jami'a daga cikinsu, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta zirin Gaza ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ma'a cewa; An fara gudanar da wani shiri na bayar da horo ga mahardata kur'ani a zirin Gaza, wanda ya kebanci mata da suka hada da daliban jami'a daga cikinsu, wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani ta zirin Gaza ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa. Babbar jami'a da ke kula da wannan shiri na bayar horo ga mahardata kur'ani mata a Gaza Ummul Haris ta bayyana cewa; yanzu haka akwai daliban jami'a mata 120 da suke halartar wannan horo, kuma za a kammala bayar da horon ne cikin watanni biyu masu zuwa.
419426