Bangaren kasa da kasa; An bude wata makarantar addinin Musulunci da wani babban masallaci da aka bai wa suna masallacin alkali Usman, wanda cibiyar turkawa ta kare hakkin biladama ta jagorancin ginawa da kuma budewa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na kungiyar kare hakkin bil adama ta IHH cewa; An bude wata makarantar addinin Musulunci da wani babban masallaci da aka bai wa suna masallacin alkali Usman, wanda cibiyar turkawa ta kare hakkin biladama ta jagorancin ginawa da kuma budewa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan cibiya ta dauki nauyin gudanar da wannan aikin ne bisa la'akari da cewa, kusan rabin mutanen kasar Kamaru musulmi ne, amma mafi yawansu suna da karancin sanin addinin da koyarwarsa, wanda kuma bude wannan makaranta da masallaci zai taimaka wajen wayar da kan musulmi da dama a kasar dangane da addinin Musulunci da kuma hakikanin koyarwarsa.
419434