IQNA

Kungiyar Hadin Kan Jami'oin Kasashen Musulmi Za Ta Gudanar Da Zamanta

18:03 - June 13, 2009
Lambar Labari: 1790429
Bangaren kasa da kasa; Kungiyar hadin kan jami'oin kasashen musulmi na shirin gudanmar da zamanta a karo na goma sha hudu a cikin mako mai zuwa, a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alriyad cewa; Kungiyar hadin kan jami'oin kasashen musulmi na shirin gudanmar da zamanta a karo na goma sha hudu a cikin mako mai zuwa, a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya. Bayanin ya ci gaba da cewa babban sakataren kungiyar kula da harkokin ilmi da ala'du na kasashen musulmi Abdulaziz bin Usman Altuwaijari shi ne zai jagoranci zaman. Daga cikin muhimman abubuwan da zaman zai dubi a kansu har da irin matsaloli da jami'oin kasashen musulmi suke fuskanta da kuma irin hanyoyin da ya kamata a bi wajen warware su tare da kawo karshensu, da kuma yadda za a karfafa hanyoyin bincike a cikin jami'oin kasashen musulmi.

419441


captcha