Bangaren kasa da kasa; An cire gungun masu sukar addinin Musulunci daga shafin internet na duniya da aka fi sani da facebook, inda aka dauki matakin korar duk wani wanda ya soke addinin Musulunci daga shiga cikin harkokin wannan shafi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Albayan cewa; An cire gungun masu sukar addinin Musulunci daga shafin internet na duniya da aka fi sani da facebook, inda aka dauki matakin korar duk wani wanda ya soke addinin Musulunci daga shiga cikin harkokin wannan shafi. Bayanin ya ci gaba da cewa, bisa la'akari dad a yadda wasu daga cikin masu tsananin gaba da addinin Musulunci suke yin amfani da wannan shafi wajen isar manufofinsu na gaba da addinin Musulunci ga sauran al'ummomin duniya, masu kula da wannan shafi sun dauki matakan taka birki ga duk wani wanda ke yin amfani da shi domin isar da manufofinsa na kiyayya da addinin Musulunci.
419468