IQNA

Kafa Babbar Cibiyar Bayar Da Gudummuwa Kan Karatun Kur'ani A Saudiya

16:19 - June 14, 2009
Lambar Labari: 1790684
Bangaren kasa da kasa;Nasir Suleiman Al'Amr shugaban kafar watsa labarai ta Almuslim ya bukaci kafa wata babbar cibiyar da za ta rika bayar da gudummuwarta kan harkokin kur'ani.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoto bayan ta nakalto daga jaridar Almadina cewa; Nasir Bin Suleiman Alamr ya gabatar da wani jawabi a lokacin wani zama kan binciken koyar da kur'ani a birnin Jidda na kasar Saudiya inda ya bayyana cewa; a halin yanzu babu ko da daya daga cikin biyoyin day a kamata su rika yin nazari da bin diddigin ayyukan koyar da kur'ani da duk wata harka da ta shafi kur'ani mai tsarki wannan littafi mai girma da daukaka kuma kafa irin wannan cibiya ba wai kawai ta taimaka a cikin gida a Saudiya a'a hatta a duniya baki daya.


419754
captcha