Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga gidan talbijin din Palasdinu cewa Taisiri altamimi ya bukaci musulmi da kiristoci da ke zaune a yankunan da Yahudawan sahayoniya suka mamaye da su kaucewa kollon wannan shiri da gidan Talbijin din haramtacciyar kasar Isra'ila ke watsawa.Yayi nuni da yadda wannan gidan talbijin ke cin mutuncin fiyayyen halitta Manzon Rahama kuma Manzon Tsira Muhammadu dan Abdullahi da kuma abubuwa masu girma da daukaka na musulunci gami da Annabi Isa (AS) Da Hadarat Maryam (AS) kuma duka wannan a wani kokari na haddasa fitina a tsakanin musulmai da kirsitoci da tada zaune tsaye.
419894