IQNA

Shugaban Jabahatul Amali Islami A Labanon Ya rasu A jiya

Bangaren kasa da kasa: Fathul Yakon babban mai yada addinin musulunci kuma shugaban jabahatul amal Islami a Labanon a safiyar jiya ne ya yi bankwana da wannan duniya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Fathi Yakon da yayi yan kwanaki yana fama da rashin lafiya a asibici ta Util Diyov a birnin Beirut babban birnin kasar Labanon ya rasu a safiyar jiya kuma an haife shi ne a shekarar 1933 a garin Trablus na Labanon yanada shahadar digirin digirgir a fanning adabin larabci da nazarin musulunci.

419952