IQNA

An Bayar Da Takardun Shedar Kammala Haradar Kur'ani Ga Dalibai A Turkiya

15:33 - June 15, 2009
Lambar Labari: 1790739
Bangaren kasa da kasa; An bayar da takardun shedar kammala hardar kur'ani ga dalibai 175 a kasar Turkiya bayan sun kammala hardar kur'ani mai tsarki, wanda aka gudanar a birnin Edrimit na kasar Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna yanakalto daga kamfanin dillancin labaran Yeni safak cewa; An bayar da takardun shedar kammala hardar kur'ani ga dalibai 175 a kasar Turkiya bayan sun kammala hardar kur'ani mai tsarki, wanda aka gudanar a birnin Edrimit na kasar Turkiya. A lokacin da ake gudanar da bukin bude cibiyar magajin garin gazi osman pasha ya bayyana cewa; kowace al'umma na da wata lama da ake gane tad a al'adunta, kuma wajibi a girmama al'adu da akidun kowace al'umma domin tabbatar da fahimtar juna da zaman lafiya da kuma abkantaka mai dorewa. Y ace yana fatan al'ummomin duniya za su amfana da wannan cibiya wajen sanin al'adu daban-daban da addinai da kuma yin nazarinsu.

419634


captcha