IQNA

Za A Gudanar Da Taron Majalisar Manyan Biranan Kasashen Musulmi

15:31 - June 15, 2009
Lambar Labari: 1790741
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da zaman majalisar manyan biranan kasashen musulmi a birnin Qazan na kasar Tatarestan, wanda zai samu halartar wakilai daga dukkanin manyan biranan musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna yanakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya cewa; Za a fara gudanar da zaman majalisar manyan biranan kasashen musulmi a birnin Qazan na kasar Tatarestan, wanda zai samu halartar wakilai daga dukkanin manyan biranan musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa za a fara gudanar da taron ne daga ranar talata mai zuwa kuma za a kammala shi a ranar laraba, wanda zai samu halartar wakilai sama da 200 daga kasashen musulmi daban-daban na musulmi, 26 daga cikinsu kuwa magaddan gari ne. Daga cikin muhimman abubuwan da za su yi dubi akansu hard a irin gudunmawar da ya kamata su bayar wajen karfafa ayyuka na yada addinin msulunci, da kuma yada al'adu na addinin musulunci. An kafa wannan majalisa ne a cikin shekara ta 1980, kuma ba gushe tana gudanar da zamanta ba a kowace shekara.

419648




captcha