Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani zaman taro kan yadda za a iya fuskantar bala'oi na dabi'a da kuma yadda za a iya fuskantarsu da ayoyin kur'ani mai tsarki a garin Sirad na kasar Turkiya, wanda ya samu halartar malamai da kuma masu bayar da fatawa na kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; An gudanar da wani zaman taro kan yadda za a iya fuskantar bala'oi na dabi'a da kuma yadda za a iya fuskantarsu da ayoyin kur'ani mai tsarki a garin Sirad na kasar Turkiya, wanda ya samu halartar malamai da kuma masu bayar da fatawa na kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa mahalrta taron sun yi dubi ne dangane da yadda ya kamata a koma ga kur'ani domin sanin tushen bala'oi na dabi'a da kuma yadda za a iya tunkararsu a mahangar kur'ani mai tsarki. Kamar yadda mahalarta taron suka jaddada cewa nauyi ne day a rataya kan malaman addini da su rika wayar da jama'a dangane da duk wasu lamurra da suka shafi hakan.
419709