Bangaren kasa da kasa; An gudanar da wani zama na musamman dangane da harkokin banki a mahangar musulunci a birnin Demascus na kasar Syria, inda aka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin kudi ga baki daya a mahangar addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana na kasar Syria cewa; An gudanar da wani zama na musamman dangane da harkokin banki a mahangar musulunci a birnin Demascus na kasar Syria, inda aka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin kudi ga baki daya a mahangar addinin musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa za a fara gudanar da taron ne daga ranar talata mai zuwa kuma za a kammala shi a ranar laraba, wanda zai samu halartar wakilai sama da 200 daga kasashen musulmi daban-daban na musulmi, 26 daga cikinsu kuwa magaddan gari ne. Daga cikin muhimman abubuwan da za su yi dubi a kansu har da irin gudunmawar da ya kamata su bayar wajen karfafa ayyuka na yada addinin msulunci, da kuma yada al'adu na addinin musulunci. An kafa wannan majalisa ne a cikin shekara ta 1980, kuma ba gushe tana gudanar da zamanta ba a kowace shekara.
420585