IQNA

Wahabiyawa Na Ingiza Yahudawan Sahyuniya Domin Kai Hari Kan Musulmi

15:04 - June 16, 2009
Lambar Labari: 1791389
Bangaren rahoto; Limamin masallacin juma'ar birnin karaci na kasar Pakistan ya bayyana cewa; wahabiyawa da ke da mummunar akida ta kafirta sauran al'ummar musulmi na da hannu wajen zuga yahudawan sahyuniya domin kai hare-hare kan al'ummar musulmi, kamar yadda sukan hada baki wasu lokutan domin kai hare-haren ta'addanci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga cibiyar ilimi ta Hauza cewa; Limamin masallacin juma'ar birnin karaci na kasar Pakistan ya bayyana cewa; wahabiyawa da ke da mummunar akida ta kafirta sauran al'ummar musulmi na da hannu wajen zuga yahudawan sahyuniya domin kai hare-hare kan al'ummar musulmi, kamar yadda sukan hada baki wasu lokutan domin kai hare-haren ta'addanci. Malamamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake wani ran gadi domin duba babban dakin karatu na babban malamin nan da aka yi a kasar Iran Ayatollah Ozma Mar'ashi Najfi. Ya ci gaba da cewa dole musulmi su fadaka daga makircikin yahudawa da wahabiyawa masu mummunar akidar kafirta musulmi.


420471




captcha