IQNA

Fathi Yakan Daya Ne Daga Cikin Fitattun Malaman Musulunci Na Zamani

15:04 - June 16, 2009
Lambar Labari: 1791393
Bangaren siyasa da zamantakewa; Babban malamin 'yan sunna kuma mai bayar da fatawa a Tripoli da arewacin Labanan ya bayyana cewa, sheikh Dr. Fathi yakan daya ne daga cikin manyan malamai na addini na zamani da suka san zamaninsu da kuma abin da ya dace da shi a zamanance.
Kamfanin dillancin labaran ikna reshen kasar labanan ya habarta cewa; a lokacin da ake gudanar da janazar babban malamin nan na kasar Labanan da Allah ya yi wa rasuwa sheikh Fathi Yakan, babban malami mai bayar da fatawa Tripoli ta kasar Labanan da kuma arewacin kasar ga mabiya mazhabobin sunna Malik She'ar ya bayyana cewa; sheikh Dr. Fathi yakan daya ne daga cikin manyan malamai na addini na zamani da suka san zamaninsu da kuma abin da ya dace da shi a zamanance. Ya ci gaba da cewa yakan ya karar da rayuwarsa baki daya wajen yi wa musulmi hidima, tare da daukaka addinin musulunci, ya yi addu'a Allah ya jikansa.

420594



captcha