Bangaren fikira da ilimi; Dole ne mabiya addinai da aka safkar daga sama su taka muhimmiyar rawa wajen taimaka ma sauran al'ummomin duniya domin fita daga kangi da matsaloli da ake fama da su da suka addabi duniya baki daya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna rehsne kasar Labanan ya habarta cewa; daya daga cikin malaman addinin kiristanci a kasar Labanan Albas Udeh ya bayyana cewa; Dole ne mabiya addinai da aka safkar daga sama su taka muhimmiyar rawa wajen taimaka ma sauran al'ummomin duniya domin fita daga kangi da matsaloli da ake fama da su da suka addabi duniya baki daya. Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin mahalarta taron masana ne da kuma malamai da suka fito daga kasashe daban-daban na musulmi da kuma na larabawa, daga cikinsu kuwa harm asana kan harkokin siyasar duniya. Babban dalilin day a jawo tattaunawar shi ne yadda wasu daga cikin malaman wahabiyawa suke fitar da fatawowin kafirta musulmi, musamman ma mabiya mazhabar shi'a.
420143