IQNA

Rasuwar Fathi Yakan Babbar Asara Ce Ga Duniyar Musulmi

15:03 - June 16, 2009
Lambar Labari: 1791396
Bangaren siyasa da zamantakewa; A cikin wani bayani da kungiyar hizbullah ta kasar Labanan ta fitar jiya ta bayyana cewa rasuwar babban malamin addinin muslunci Fathi Yakan babbar asara ce ga dukkanin duniyar musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Labanan ya habarta cewa; A cikin wani bayani da kungiyar hizbullah ta kasar Labanan ta fitar jiya ta bayyana cewa rasuwar babban malamin addinin muslunci Fathi Yakan babbar asara ce ga dukkanin duniyar musulmi. a lokacin da ake gudanar da janazar babban malamin nan na kasar Labanan da Allah ya yi wa rasuwa sheikh Fathi Yakan, babban malami mai bayar da fatawa Tripoli ta kasar Labanan da kuma arewacin kasar ga mabiya mazhabobin sunna Malik She'ar ya bayyana cewa; sheikh Dr. Fathi yakan daya ne daga cikin manyan malamai na addini na zamani da suka san zamaninsu da kuma abin da ya dace da shi a zamanance. Ya ci gaba da cewa yakan ya karar da rayuwarsa baki daya wajen yi wa musulmi hidima, tare da daukaka addinin musulunci, ya yi addu'a Allah ya jikansa.


420331




captcha