IQNA

An Gudanar Da Janazar Shugaban Kungiyar Amal Islami A Tripoli

15:03 - June 16, 2009
Lambar Labari: 1791398
Bangaren siyasa da zamantakewa; A jiya ne aka gudanar da janazar babban malamin addinin musulunci kuma jagoran kungiyar Amal Islami Sheikh Dr Fathi Yakan a birnin Tripoli da ke arewacin kasar Labanan, bayan da Allah ya yi masa cikawa a birnin Beirut.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar labanan ya habarta cewa; A jiya ne aka gudanar da janazar babban malamin addinin musulunci kuma jagoran kungiyar Amal Islami Sheikh Dr Fathi Yakan a birnin Tripoli da ke arewacin kasar Labanan, bayan da Allah ya yi masa cikawa a birnin Beirut. Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin malamai dam asana da 'yan siyasa daga sassa daban-daban na kasar Labanan sun halarci wannan janaza, inda aka rufe shi a makabartar Babul ramal da ke garin Tripoli. Fathi Yakan ya rasu yana da shekaru 76 a duniya, ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya. Ya shahara wajen kare gwagwarmayar al'ummar Labanan a karkashin jagorancin hizbullah.


420316


captcha