IQNA

Dole Ne Malamai Su Hana Fitar Da Fatawoyin Kafirta Musulmi

15:03 - June 16, 2009
Lambar Labari: 1791399
Bangaren kasa da kasa; Wajibi ne da ya rataya kan dukkanin malamai da masana musulmi da dauki dukkanin matakan da suka dace domin hana fitar da fatawoyi na kafirta musulmi da wahabiyawa masu tsattsuran ra'ayi ke yi, domin kuwa ci gaba da yin hakan zai haifar da babbar baraka tsakanin musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar hadaddiyar daular larabawa cewa; shugaban kungiyar hada kan al'ummar Musulmi Kamal Halbawi ya bayyana cewa; Wajibi ne da ya rataya kan dukkanin malamai da masana musulmi da dauki dukkanin matakan da suka dace domin hana fitar da fatawoyi na kafirta musulmi da wahabiyawa masu tsattsuran ra'ayi ke yi, domin kuwa ci gaba da yin hakan zai haifar da babbar baraka tsakanin musulmi. Ya ci gaba da cewa rarraba tsakanin musulmi babu wani wanda za ta amfanar sai masu gaba da addinin musulunci, kuma ya zama wajibi a kawo karshen hakan.

420628



captcha