Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alakhbar cewa; An fara gudanar da wani baje kolin kayayyakin fasaha na addinin musulunci a kasar Amurka, wanda kungiyoyin musulmi da ke birnin New York suka dauki nauyin shiryawa da gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin abubuwan da aka baje kolinsu a wurin har da alluna da suke dauke da rubutun hannu, wanda aka yi da larabci da kuma kawata su da ababen ado, bayan haka kuma an nuna hotunan wasu daga cikin kayan tarihin musulunci da ke wasu kasashe musamman ma kasashen yankin gabas ta tsakiya. Haka nan kum an nuna hotunan wurare na tarihin musulunci da ke Makka da Madina da sauran muhimman wurare da ke cikin saudiya Syria da sauransu.
420629