IQNA

An Bude Wani Masallaci A Sansanin Palastinawa A Kasar Jordan

15:02 - June 16, 2009
Lambar Labari: 1791402
Bangaren siyasa da zamantakewa; An bude wani babban masallaci a wani sansanin palastinawa 'yan gudun hijira da ke yankin Souf a kasar Jordan, wanda hukumar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Jordan ta dauki nauyi ginawa.
Kamfanin dillanicn labaran Ikna ya reshen kasar Jordan ya habarta cewa; An bude wani babban masallaci a wani sansanin palastinawa 'yan gudun hijira da ke yankin Souf a kasar Jordan, wanda hukumar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Jordan ta dauki nauyi ginawa. Babban daraktan ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Jordan shi ne ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Amman fadar mulkin kasar Jordan, ya ci gaba da cewa bangarori da dama sun taimaka wajen bayar da gudunmawa wajen ganin ginin masallacin ya kammala, daga cikin kuwa har da kungiyar nan ta bayar da taimako ta kasar Kuwait.

419316










captcha