Bangaren kasa da kasa; An gudanar da bangare na karshe na gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da ta kebanci mata a kasar Turkiya, wanda babbar cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta birnin Aidin na kasar Turkiya ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a sassa daban-daban na kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Turkya cewa; An gudanar da bangare na karshe na gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da ta kebanci mata a kasar Turkiya, wanda babbar cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta birnin Aidin na kasar Turkiya ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a sassa daban-daban na kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa; wannan gasa ta samu halartar mahardata da makaranta kur'ani mata daga sassa daban-daban na kasar Turkiya, inda suka kara da juna ta fuskacin harda da kuma karatu wato kira'a, da kuma karatun ka'idojin karatun kur'ani mai tsarki wato tajwidi, wadanda suka lashe gasar sun samu kyautuka.
421084