IQNA

Za A Gudanar Da Wata Tattaunawa Tskanin Addinai A Senegal

16:00 - June 17, 2009
Lambar Labari: 1791899
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wata tattaunawa tsakann mabiya addinai a kasar Senegal, wadda cibiyar kula da harkokin addinai da al'adu ta Konarad ta shirya gudanarwa tare da hadin gwiwa tsakaninta da jami'ar Sheikh Anta Diov a birnin Dakar fadar mulkin kasar ta Senegal.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Senegan APS cewa; Za a gudanar da wata tattaunawa tsakann mabiya addinai a kasar Senegal, wadda cibiyar kula da harkokin addinai da al'adu ta Konarad ta shirya gudanarwa tare da hadin gwiwa tsakaninta da jami'ar Sheikh Anta Diov a birnin Dakar fadar mulkin kasar ta Senegal. Taron wanda zai samu halartar malamai dam asana daga kasashen musulmi da ma na turai gami da Asia, Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar wakilai kimanin 600 daga kasashen sama da talatin da biyar, inda za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinai ta yadda za su zauna da juna lafiya baki daya.

421131
captcha