IQNA

Jordan Ta Bayar Da Kyautar Kur'anai Ga Jami'ar Palastinu

16:03 - June 17, 2009
Lambar Labari: 1791901
Bangaren kur'ani; Gwamnatin kasar Jordan ta bayar da kyautar kur'ani mai bugun ibril guda dari ga jami'ar palastinu da ke birnin Ramalla na yankin palastinu, domin karfafa daliban jami'a wajen mayar da hankali ga karatun kur'ani mai tsarki da kuma yin aiki da koyarwarsa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran palastinu ma'a cewa; Gwamnatin kasar Jordan ta bayar da kyautar kur'ani mai bugun ibril guda dari ga jami'ar palastinu da ke birnin Ramalla na yankin palastinu, domin karfafa daliban jami'a wajen mayar da hankali ga karatun kur'ani mai tsarki da kuma yin aiki da koyarwarsa. Bayanin ya ci gaba da cewa ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Jordan ce ta dauki nauyin tanadar wadannan kur'anai domin karfafa gwiwar dalibai wajen komawa ga karatun kur'ani da kuma yin aiki da koyarwarsa. Bayanin ya ci gaba da cewa adadin kur'ani ya kai 100 dukkaninsu kuma bugun ibril, wanda aka kaddara shi da kudi masu tsada.

420803

captcha