Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da wani bayar da horo na karatun kur'ani mai tsarki ga nakasassu a Turkiya, da zai hada da bude azuzuwa na koyar da karatun kur'ani da ma sauran ilmomin addini gami da sanin rayuwa ta zamantakewa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; Za a fara gudanar da wani bayar da horo na karatun kur'ani mai tsarki ga nakasassu a Turkiya, da zai hada da bude azuzuwa na koyar da karatun kur'ani da ma sauran ilmomin addini gami da sanin rayuwa ta zamantakewa. Bayanin ya ci gaba da cewa daya daga cikin malaman addinin kasar Osman Demir a ta bakin mai Magana da yawunsa ya bayyana cewa wannan na daya daga cikin kokarin da aka fara yi domin ilmantar da nakasassu ilmomin addinin musulunci musammanma bangaren ilmomin kur'ani mai tsarki, da sauran ilmomi na fikihu da hukunce-hukuncen addini.
421490