IQNA

Za A Gudanar Da Wani Taro Kan Addinin Musulunci A Scotland

14:58 - June 18, 2009
Lambar Labari: 1792096
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro a birnin Adinboro na kasar Scotland dangane da addinin musulunci, da kuma bayanai kan hakikanin koyarwarsa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Islam festival cewa; Za a gudanar da wani zaman taro a birnin Adinboro na kasar Scotland dangane da addinin musulunci, da kuma bayanai kan hakikanin koyarwarsa. Bayanin ya ci gaba da cewa a wajen wannan taron za a gudanar da muhimman abubuwa da dama da suka danganci addinin musulunci, da hakan ya hada da bayani kan hakikanin koyarwar musulunci ga bil adama maimakon farfagandar da ake yadawa da nufin kawo cikas ga yada tunanin musulunci. Haka nan kuma a wajen taron za a bayar da horo na 'yan kwanaki dangane dangane da ilmomin kur'ani, kamar yadda za a bude wani baje koli na kayan tarihin musulunci a wurin.

421509
captcha